8 Disamba 2019 - 05:27
Amurka Ta Sako Wani Masanin Iran

A yau Asabar ne Dr. Mas’ud Sulaimani wanda aka sake shi ya isa birnin Zurich inda ya sami tarbar ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Muhammad jawad Zarif.

(ABNA24.com) Majiyar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa; Dr. Sulaimani wanda malamin jami’a ne an tsare shi a Amurka fiye da shekara daya.

Sakin Sulaimani ya zo ne a daidai lokacin da majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta amince da sakin wani Ba’amurke, Jao Wang sanda aka tsare shi anan Iran bayan da aka same shi da laifin leken asiri.

Ministan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Muhammad Jawad Zarif ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; Ina matukar farin ciki cewa Dr. Mas’ud Sulaimani da Mr. Wang za su hadu da iyalansu ba da jimawa ba. Kuma muna yin godiya ga gwmanatin Swissland wacce ta taka rawa a cikin lamarin.”




/129